1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin warware matsalar Fari a Somaliya

August 25, 2011

Ƙungiyar tarayyar Afirka ta buɗe taron tattauna matsalar fari a gabashin Afirka

https://p.dw.com/p/12Nc2
Shugaban tarayyar Afirka (AU), Teodoro Obiang NguemaHoto: AP

Ƙungiyar tarayyar Afirka AU ta buɗe babban taron masu bayar da agaji game da matsalar fari dake addabar ƙasar Somaliya. Ƙungiyar ta buɗe taron ne a hedikwatar ta dake birnin Addis Ababa, fadar gwamnatin ƙasar Ethiopia. A cewar shugaban hukumar tarayyar Afirka Jean Ping, fiye da mutane miliyan 12 ne matsalar fari ke addaba a yankin gabashin Afirka, waɗanda kuma ke zaune a ƙasashen da suka haɗa da Somaliya, Kenya, Ethiopia, da Eritrea da kuma Djibouti.

Ƙiyasin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi dai ya nunar da cewar ana neman fiye da dalar Amirka miliyan dubu ɗaya domin shawo kan matsalar, wadda ta fi tsanani a ƙasar Somaliya, inda kimanin ƙananan yara dubu 400 ke fuskantar tsananin nyunwa. Wannan dai shi ne fari - mafi muni da yankin ya yi fama da shi cikin shekaru 60 da suka gabata.

A cikin jawabin da ta yiwa taron, wanda ke samun halartar shugabannin ƙasashen Afirka huɗu kaɗai, ƙaramar sakataren da ta wakilci sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya a taron, Dakta Aisha-Rose Migiro ta buƙaci duniya ta ɗauki mataki cikin gaggawa:

" Ta ce, saboda munin matsalar akwai buƙatar mu hanzarta ɗaukar matakin gaggawa domin shawo kanta. A Somaliya kaɗai fari ya yi muni a yankin kudanci-ciki kuwa harda Mogadishu, babban birnin ƙasar, kuma akwai yiwuwar zai yaɗu zuwa sauran sassan ƙasar nan da makonni huɗu zuwa shidda dake tafe. Dubun dubatan mutane ne suka mutu, kuma akwai kimanin Somaliyawa miliyan ukku da dubu 200 da ke fuskantar matsalar tsananin nyunwa adadin da kuma ya haɗa da mutane miliyan biyu da dubu 800 a yankin kudancin ƙasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar