1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ci gaba da shari'ar kashe tsohon shugaban Burkina Faso

Suleiman Babayo ATB
October 25, 2021

An koma shari'ar bisa tuhumar mutane 14 da kisan tsohon shugaban Burkina Faso Thomas Sankara shekaru 34 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/429iw
BdTD | Burkina Faso
Hoto: AFP

A wannan Litinin aka koma shari'a a kasar Burkina Faso na mutane 14 da ake zargi da kashe tsohon shugaban kasar Thomas Sankara shekaru 34 da suka gabata. Wata kotun soja da ke birnin Ouagadougou fadar gwamnatin kasar ke sauraron bahasi kan tuhume-tuhumen da ake yi wa mutanen.

Ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 1987 aka halaka Marigayi Sankara da wasu mutane 12 cikin wani juyin mulki na soja, inda na hannun damarsa Blaise Compaore ya kwace madafun ikon kasar da ke yankin yammacin Afirka, kuma yanzu haka Compaore yana cikin mutanen da ake tuhuma amma a bayan idonsa domin yana kasar Cote d'Ivoire tun shekara ta 2014 lokacin da zanga-zangar adawa da sake sauya kundin tsarin mulki ta kawo karshen gwamnatinsa ta shekaru 27.

Ita wannan shari'a kan tabbatar da neman hukunta wadanda suke da hannu wajen kashe Marigayi Thomas Sankara tana daukan hankali a ciki da wajen kasar ta Burkina Faso.