A Burkina Faso an yi jana'izar mazajen da suka fadi a fagen dagga
December 2, 2014Talla
Jama'ar waɗanda suke riƙe da juna hannu da hanu a ciki har'da shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Michel Kafando tare da fira ministan Lt. Col. Isaac Zida.Sun taru a wani dandali da aka sake farfaɗo da sunansa tun lokacin mulkin Thomas Sankara wato danalin juyin juya hali.
Inda daga can ne aka ɗauki gawarwakin mamanta a cikin wata motar soji zuwa maƙabarta.Mutane 24 suka mutu a zanga-zangar da aka yi a ƙarshen watan Oktoban jiya a ƙasar ta Burkina Faso