1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A shekaru 30 Somaliya na karbar taron koli

Yusuf BalaSeptember 13, 2016

A ranar Talatan nan kasar Somaliya ta karbi bakuncin taron koli na shugabanni daga kasashen Afirka abin da ke zama na farko cikin shekaru 30.

https://p.dw.com/p/1K1Wa
München Sicherheitskonferenz - Hassan Sheikh Mohamud, Präsident Somalia
Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na SomaliyaHoto: Reuters/M. Dalder

A ranar Talatan nan kasar Somaliya ta karbi bakunci na taron koli na shugabanni daga kasashen Afirka, abin da ke zama na farko cikin shekaru 30, wani abin alfahari ga al'ummar kasar da a shafukan intanet ke nuna farincikinsu bayan gwamman shekaru da kasar ta kwashe tana fama da aiyukan ta'addancin mayakan al-Shabab, wanda aiyukan tashin bama-bamansu ke mamaye shafukan na intanet a kasar.

An dai tsaurara matakan tsaro a kasar wacce ta karbi bakuncin shugabanni irin su Uhuru Kenyatta na Kenya da Yoweri Museveni na Yuganda da Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn.

Shugaban kasar Sudan dai Omar al-Bashir ya ce ba zai halarci taron ba duk kuwa da mika masa goron gayyata kamar yadda ministan harkokin wajen Somaliya Abdisalam Omer ya tabbatar.

A cewar mazauna biranen kasar dai ana bukukuwan sallah babba cikin yanayi na tsauraran matakan tsaro.