Mace mai sana'ar kanikanci a Abuja
January 8, 2020A Najeriya ba kasafai ake samun mata su shiga sana'ar kanikanci wato gyaran mota ba, to sai dai ga Joyce Longtang Daser ta cire tuta, inda ta rungumi wannan sana'a a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Yanzu ma tana da 'yan mata 30 da ke karkashinta suna koyon sana'ar a matsayin hanyar dogaro da kai.
Da mutum ya je shagonta zai iske matashiya Joyce Longtang Daser Adam ta wargaje mota tana kokarin hada injinta, ga wasu 'yan mata zagaye suna koyon aiki. Duk da cewa ta yi karatu har matakin digiri bai sa Joyce ta rungume hannu tana jiran aiki ba. Shin me ya bata sha'awa ta fara wannan sana'a ta gyran mota da har ta kai ga bude makeke shago haka a birnin Abuja?
"Na karanta ilimin gyaran injuna wato Mecahnical Engineering a jami'a. Da yake babu aiki a Najeriya, sai na koyi aikin hannu lokaci da aka tura ni koyon aiki a wata masana'anta."
Kasancewar Joyce mace da ke sana'ar gyaran mota da bisa al'ada maza ne suka mamayeta a Najeriya, ko akwai kalubalen da take fuskanta?
"Idan maza suka kira suna neman su kawo mota a gyara musu, in sun ji muryar mace a kan waya sai su ce in bawa maigidana waya suna son su kawo mota ya gyara musu. Ama sai in ce musu a ni ce mai gyaran motar. Wato nke nan har yanzu a Najeriya ba a saba da ganin mace mai sana'ar kanikanci ba."
Akwai dai 'yan mata da ke koyon sana'ar gyaran mota a karkashin Joyce Longtang. Juliet Moses na daya daga cikinsu wadda ta ce dalilin da ya sa take koyon aikin gyaran mota shi ne tana sha'awar ta yi aikin da ba a saba ganin mata na yi a Najeriya ba.
Ita kuwa Priscila Godwin matashiya da shekarunta 20 ta yi nisa a sana'ar gyaran mota, shin wane kalubale ta fuskanta?
Aikin gwamnati shi yafi daukan hankali matsa irin Joyce Longtang musamman yadda ta yi karatu har matakin digiri, amma ta ce ko da za ta samu aikin gwamnati yanzu ba za ta yi watsi da sana'ar gyaran mota ba.
Da wannan himma da matasa mata ke yi, na nuna sauyi na sana'oin da mata ke runguma a Najeriya domin dogaro da kai.