1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sana'ar gyaran gashi a Abuja

Zainab Mohammed Abubakar MNA
March 13, 2019

Justina Gabriel matashiya ce da ke harkar gyaran gashi a birnin Abuja. Tun bayan kammala karatunta matashiyar ta kama wannan sana'a, inda sannu a hankali har ya kai ta ga bude shago tare da horar da wasu matasan.

https://p.dw.com/p/3Ew3v
Elfenbeinküste Frau bei Friseur in Abidjan
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Matashiyar wadda aka fi sani da suna "Mummy" ta shahara wajen yin kitso da gyaran gashi da duk wasu nau'o'in abubuwan da suka danganci gyaran kan mace da farcen hannu da na kafa.

Justina Gabriel ta ce kamar da wasa ta fara sana'ar yin kitso a shekara ta 2004, sannu a hankali har ta kai zuwa wannan lokaci, inda ta kware har tana baiwa wasu matasa 'yan uwanta horo kan yadda za su gyara jikin mata kama daga gashi zuwa farcen hannu da na kafa.

Ta shaidar da cewar wannan sana'a sai dai san barka saboda irin alfanu da ta samu a ciki a 'yan shekaru da suka gabata.

Da aka nemi sanin ko shin idan yanzu Justina ta samu aikin gwamnati za ta yi watsi da wannan shago nata ta koma ofis? Sai ta ce ko kadan ba za ta iya barin wannan sana'a tata ba, domin kwalliya na biyan kudin sabulu.

Sai dai kamar kowa ce sana'a da ke tafiya da zamani, batun gyaran gashi ko jikin mata wata aba ce da kullum ke samun sauyi kuma ga tsada, kuma dole ne ka tafi da wannan sauyin, a cewar matashiyar.