1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Abdullahi Tanko Bala LMJ
November 20, 2020

Batun zabe a Burkina Faso da yakar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da rikicin da ake fama da shi a Habasha, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/3ld62
Burkina Faso Präsident Roch Marc Christian Kabore
Shugaba Roch Marc Christian Kabore na Burkina FasoHoto: Reuters/A. Sotunde

A sharhinta na wannan mako, jaridar die Tages Zeitung wadda ta yi tsokaci kan zaben shugaban kasa a Burkina Faso mai taken: Makomar 'yan ta'adda. Shin ko ya dace a tattauna da kungiyoyi masu ikrarin jihadi? A wannan Lahadin ne ake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a Burkina Faso. Shugaba mai ci Roch Marc Christian Kabore na jam'iyyar MPP na fafatawa da madugun adawa Zephirin Diabre mai shekaru 61 na jam'iyyar UPC. Batun samar da aiki ga matasa da kuma koma bayan tattalin arziki, su ne suka mamaye muhawarar zaben a wannan karon.

Sulhu ne mafita a yaki da ta'addanci?

Bugu da kari Burkina Faso ta kasance a tsakiyar yaki da 'yan ta'adda. A ra'ayin shugaban kasar amfani da makami bai taba kawo sulhu ga ayyukan 'yan ta'adda ba, a saboda haka ya ce tattaunawa ita ce mafita. A Burkina Faso dai mayakan jihadin ba daga arewacin Afirka ko Gabas ta Tsakiya ake shigo da su ba, 'yan kasa ne a cikin gida sai kuma in ta yi kamari 'yan kasar Mali. Shugaba Kabore ya sha fada a baya cewa, a karkashin mulkinsa zai kawo karshen masu tayar da kayar baya. Jaridar ta ce batun tsaro da zaman lafiya su ne muhimman al'amuran da suka shige wa mutane da dama gaba a Burkina Faso. Sai dai kuma ko wace irin mafita ko masalaha za a samu, yana da muhimmanci ga wanzuwar makomar kasar a gaba.

Kongo Mbandaka Impfung gegen Ebola
Tasirin rigakafin Ebola a KongoHoto: Getty Images/AFP/J.D. Kannah

Jerin alluran rigakafi sun kawo karshen Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo, wannan shi ne taken jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce a tsakiyar wannan makon an kawo karshen cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo bayan shafe watanni shida ana allurar rigakafi a kasar baki daya. Ministan lafiya na kasar da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, sun bayar da cikakken tabbaci a kan haka. Cutar ta bulla ne a Arewa maso Yammacin kasar a birnin Mbandaka a gabar kogin Kongo, jim kadan bayan da aka sami barkewar annobar a gabashin kasar da aka shafe shekaru biyu ana fama, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 2,000.

Dole kanwar naki

Mutane fiye da 40,000 aka yi wa rigakafin a shirin allurar da ya sami tallafin kungiyar Gavi. Jaridar ta ce idan ba a manta ba, a shekarar 1976 cutar Ebola ta fara bulla a yankin Zaire, kamar yadda ake kiran kasar a wancan lokaci. Tun daga wannan lokaci, an samu barkewar annoba a Kongo har sau 11 fiye da kowace kasa. Mafi munin annobar da aka gani a yammacin Afirka shi ne a watan Maris na shekarar 2014, inda cutar ta halaka mutane fiye da 28,000 yayin da  kuma ta yadu a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo. A karshe jaridar ta ce fata na gari lamiri, yayin da a baya marasa lafiya da dama suka rika kauracewa maganin asibiti suke bin masu maganin gargajiya saboda suna ganin cutar a matsayin wata la'anta, a yanzu ana iya cewa kimiyya ta yi nasara.
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhinta ne akan kasar Habasha. Ta ce yakin Habasha ya fadada. An shigar da Iritiriya cikin rikicin yankin Tigray da ke gwagwarmayar ballewa don samun 'yancin kai. Jaridar ta ce karuwar tashin hankali tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan yankin Tigray da ke neman ballewa, talakawa sune ke dandana kudarsu.

Tigray-Konflikt | Flüchtlinge im Sudan
Al'umma cikin halin tasku a HabashaHoto: ASHRAF SHAZLY/AFP/Getty Images

Jaridar ta yi waiwayen baya, inda ta ce har izuwa 1993 ana yi wa yankin mulki da karfin tuwo, kamar yadda aka gani daga shugaba Isayas Afewarke. Ko da yake jam'iyyar TPFL tare da kawayenta na Iritiriya, sun murkushe gwamnatin kwamunisanci ta Addis Ababa a 1991, amma har bayan yakin samun 'yancin kai dangantaka tsakanin kasashen biyu makwabtan juna ta yi tsami. Wannan kuwa a cewar jaridar, ba ya rasa nasaba da mulkin kama-karya na shugaba dan Tigray na wancan lokaci Meles Zenawi da tawagarsa.