1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus(16-04-21)

Abdullahi Tanko Bala AH
April 16, 2021

Batun muhawara da ake tafkawa a kasashen duniya a game da inganci allurar rigakafi ta Astrazeneca da kuma tsawaita wa'adin mulki da shugaban Somaliya ya yi, su ne batutuwan da suka dauki hankalin Jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3s82G
AstraZeneca Covid-19 Impfung
Hoto: Yui Mok/PA Wire/empics/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta yi sharhinta a kan dogaron Afirka wajen shigo da allurar rigakafin corona daga kasashen waje. Jaridar ta buga misali da Afirka ta Kudu wadda ministanta na lafiya Zweli Mkize ya gabatar da tsarin yi wa 'yan kasar allurar rigakafin corona, bada jimawa ba kuma ya sanar da dakatar da shirin a wannan karon akan allurar Johnson & Johnson wanda Amirka ta dakatar da yin sa saboda matsalar daskarewar jini da aka samu. Jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce dakatar da yin rigakafin wani karin koma baya ne ga Afirka ta kudu. Kawo yanzu dai ita ce kadai kasar Afirka da ta gudanar da allurar ta Johnson Johnson. A watan Fabrairu ba zato ba tsamani da jingine allurar AstraZeneca saboda daskarewr jini. A wancan lokaci masana kimiya sun hakikance cewa allurar bata da tasiri akan nau'in cutar corona da aka samu a kasar. Mutanen da aka yi wa rigakafin kawo yanzu ba su wuce mutum 300,000 ba yawancinsu ma'aikatan lafiya. Koda yake gwamnatin ta ce dakatarwar na wucin gadi ne domin tantance bayanai daga Amirka kan musabbabin daskarewar jini da aka samu a wasu da aka yiwa rigakafin.

Kasashen duniya na yin dari-dari da allurar AstraZeneca

Weltspiegel 12.04.2021 | Corona | Taiwan Taoyuan | Impfung
Hoto: Ann Wang/REUTERS

Sai dai kuma Afirka ta kudu ba ita ce kadai kasar Afirka da allurar rigakafin ke tafiyar hawainiya ba, a kasashen Turai da Amirka ma an sami haka. A 'yan watannin da suka wuce martanin al'umma sun cika shafukan sada zumunta inda suke adawa da yadda wasu suka yi kakagida musamman kasashe da suka samar da rigakafin a waje guda kuma da yadda wasu ke dari-dari da karbar allurar. A baya- bayan nan shugabar kungiyar ciniki ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta soki lamirin abin da ta kira dogaro mara hujja na rashin samar da maganin ga kasashe masu raunin tattalin arziki inda tace kashi daya ne cikin dari na kasashen Afirka suka sami rigakafin idan aka kwatanta da arewacin Amirka da ta sami kashi 40 cikin dari na allurar. Jaridar ta ce babban abin dubawa dai shi ne nahiyar Afirka ta dogara ne kacokam wajen shigo da maganin daga waje. A yanzu dai ana ta kiraye kiraye a samar da kamfanin hada magungunan a Afirka. Yayin da kungiyar tarayyar Afirka ke kokarin ganin an rage dogaro wajen shigo da alluraran daga waje daga kashi 99 cikin dari zuwa kashi 40 cikin dari nan da shekara ta 2040.

Shugaban Somalia ya tsawaita wa'adin mulkinsa ba tare da zabe ba. Wannan shi ne taken sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi. 

Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed
Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi MohamedHoto: Vladimir Smirnov/TASS/imago images

Jaridar ta ce a lokacin da Donald Trump yake kan karagar mulki Jakadan Amirka a Mogadishu ya baiwa shugaban Somalia hula hana sallah mai launin shudi da fari da akka rubuta yunkura domin sake farfado da kasar Somalia. To amma shekaru biyu bayan nan fatar sake gina kasarta Somalia bai da armashi ko kusa. Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed ya tsawaita wa'adin mulkinsa da shekaru biyu ba tare da zabe ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Wannan ya harzuka 'yan adawa ya kuma fusata kasashen duniya. Amirka da tarayyar Turai sun yi kakkusar suka ga wannan mataki.Zanga-zanga ta barke fargaba ta cika zukata game da yiwuwar sake aukuwar tashin hankali. Somalia ta sami kanta cikin rashin zaman lafiya tun bayan da aka kawar da gwamnatin shugaban kama karya Mohammed Siad Barre a 1991. Tambayar ita ce Shin shugaban Mohammed Abdullahi Mohammed ya kama hanyar zama alamar faduwar nasara da koma baya ne a Somaliya? Ya dai yi alkawarin cikin shekaru biyu masu zuwa zai samar da inghantaccen tsarin dimukuradiyya da wanzuwar cigaba a kasar.