Afirka a shekara ta 2014
An cinnawa ginin majalisar dokokin Burkina Faso wuta, Afirka ta Kudu ta cika shekaru 20 da fara mulkin dimokaradiyya, a Najeriya ana cikin damuwar sace 'yan matan Chibok da 'yan Boko haram suka yi. 2014 ke nan a Afirka
Annobar cutar Ebola ta addabi yankin yammacin Afirka
A watan Maris na 2014 ne aka fara samun mai cutar Ebola a kasar Guinea. Nan take kwayar cutar ta yadu zuwa makwabtanta kasashen Laberiya da Saliyo, da taimakon rashin kula da kuma karancin kayan kula da kiwon lafiyar al'umma. An samu rahoton cutar a wasu kasashen Afirka da Turai har ma da Amirka. Zuwa watan Disamba mutane sama da dubu 17 sun kamu da cutar, mafi yawansu a nahiyar Afirka.
Ebola ta wargaza rayuwar al'umma
A yayin da nahiyar Turai ke kokarin kula da al'ummarta da suka kamu da cutar Ebola cikin kwarewa, a yammacin Afirka suna kokarin samun agaji da cibiyoyin kebe masu cutar da likitoci domin yakar Ebola. Afirka ta yamma na fatan samun magani. Annobar Ebola ta kassara tattalin arzikin Laberiya da Saliyo da kuma Guinea. Ta mayar da yara marayu. Tuni aka yi watsi da cututtuka irinsu Malaria da Typhoid.
Sudan ta Kudu. Yakin basasa a jaririyar kasa
Kimanin shekara guda kenan ana Fama da rikici a Sudan ta Kudu. Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da kokarin yi masa juyin mulki a watan Disamba na shekara ta 2013. Sama da mutane miliyan guda ne suka yi hijira zuwa kasashe makwabta domin kaucewa yakin, yayin da wasu dubbai kuma suka hallaka. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta sai dai ba ta je ko ina ba ta wargaje.
Najeriya: 'Yan ta'adda sun sace 'yan mata 'yan makaranta
A ranara 16 ga watan Afirilu ne 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata sama da 200 a garin Chibok a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Wannan ya janyo yin gangami ta kafafen sadarwa na zamani a kasa da kasa mai taken #BringBackOurGirls. 'Yan Najeriya na zargin gwamnati da kin tabuka komai duk da cewa mahukuntan kasar sun san inda 'yan matan suke, sai dai har yanzu sun gaza ceto su.
Najeriya: Boko Haram na cin karenta ba bu babbaka
Zuwa karshen watan Dissamba, kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa, sun kashe daruruwan mutane. Kungiyar ta kwace iko da wasu manyan garuruwa a arewacin Najeriya kamar su Gwoza. Shugaba Goodluck Jonathanya nemi da a kara dokar ta baci da ya sanya a jihohin arewa maso gabashin kasar a watan Mayun 2014. A yanzu haka Jonathan ya ce zai sake tsayawa takara a 2015.
Sake gina Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Bayan kashe mutane a Disambar 2013, A shekara ta 2014 an samu sabon fata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.Catherine Samba-Panza ta karbi mulki daga shugaban 'yan tawaye Michel Djotodia. Al'ummar kasar basu amsa kiran ta na sulhu ba. Dakarun kungiyar Tarayyar Turai da kungiyar Hadin kan Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya na kokarin hana samun rikici tsakanin 'yan Seleka da anti-balaka.
Afirka ta Kudu: Shekaru 20 bayan wariyar launin fata
Shekaru 20 bayan zabe na farko da aka yi a Afirka ta Kudu, siyasar kasar ta shiga cikin rudani. Shugaba Jacob Zuma na fuskantar suka daga 'yan adawa da ma jam'iyyarsa ta ANC bisa zarginsa da almubazzaranci da kudaden al'umma da rashin iya gudanar da mulki. Jam'iyyar ANC ta baiwa 'yan Afirka ta Kudu da dama kunya. Babu aikinyi ga matasa, tattalin arzikin kasar kuma na cikin garari.
Samun nasarar Dennis Kipruto a Berlin
Bayan tsahon sa'a guda yanaa gudu, ya fuskanci abubuwa na tafiya dai-dai. A ranar 24 ga watan Afrilu, dan kasar Kenya Dennis Kimetto ya kammala gasar gudun fanfalake a Berlin cikin sa'oi biyu da mintuna biyu da sakan 57 inda ya lashe kyaututtuka. Gabanin fara tseren, mai shkerau 30 a duniya da ya shiga gasar a karo na farko ya ce yana son Berlin, ta yiwu hakan ya taimaka masa wajen samun nasara.
An gujewa tashin hankali tare da gudanar da zabuka a Mozambik
A farkon shekara Mozambik na daf da fadawa cikin yakin basasa. Jam'iyyar adawa ta RENAMO ta bukaci magoya bayanta su dau makamai. Sai dai an cimma sabuwar yarjejeniyar sulhu a karshe tsakaninsu da gwamnati. Wannan ya ba da damar yin zaben shugaban kasa a watan Oktoba. Kuma Filipe Nyusi na jam'iyya mai mulki ta FRELIMO ne ya lashe zaben.
Mali: Har yanzu ba a shawo kan rikici da 'yan tawaye bai kare ba
Zaben shugaban kasa da aka yi a Mali a watan Satumbar shekara ta 2013 bai magance rikicin da kasar ke fuskanta ba. A watan mayun 2014 'yan tawayen Abzinawa sun mamaye arewacin garin Kidal, tare kuma da kin janye bukatarsu ta samun 'yancin cin gashin kai. Tattaunawa tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawayen karo na uku da aka yi a watan Nuwamba ta watse ba tare da cimma matsaya ba.
Burkina Faso ta bukaci komawa kan turbar dimokaradiyya
Shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore da ya kwashe shekaru 27 a kann karagar mulki na son yin tazarce ta hanyar yin kwaskwarima ga Kundin tsarin mulkin kasar. Al'ummar kasar sun yi wa Compaore tawaye tare da tilasta masa tserewa zuwa kasar Cote d'Ivoire. Sojojin kasar sun kafa gwamnatin rikon kwarya tare da bukatar ta shirya zabe a shekara ta 2015 mai zuwa.
Denis Mukwege ya lashe kyautar jarumtaka ta majalisar Tarayyar Turai
'Yan majalisar Tarayyar Turai sun kadu a yayin da Dr Denis Mukwege ke labarta irin aikin da ya ke a asibitin Panzi da ke garin Bukavu a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango. Kwararren likitan mata, na duba matan da aka yi musu fyade da kuma kaciya a yayin yakin basasa. Majalisar Tarayyar Turan ta girmama shi da kyautar jarumtaka sakamakon kare 'yanci da kuma hakkin dan Adam.
Kenya: Kotun ICC ta ajiye tuhumar da ta ke yiwa Uhuru Kenyatta
Kotun kasa da kasa mai hukunta masu aikata laifukan yaki dake birnin "The Hague" ta yi watsi da tuhumar da take yi wa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta. Babbar mai gabatar da kara ta ajiye tuhumar da ake maa ta aikata laifukan yaki bisa rashin wadatattun shaidu da za ta gabatarwa da kotun. Ana zargin Kenyatta ta laifin fyade da cin zarafi da kuma kisa bayan zaben shekara ta 2007 a Kenya.
Al-Shabab: Hare-hare a Somalia da Kenya
'Yan ta'addan al-Shabab na kasar Somaliya sun fadada hare-harensu zuwa kasar Kenya dake makwabtaka. A shekara ta 2014 mutane 200 ne suka hallaka a hare-hare sama da 25 da kungiyar ta kai. Al-Shabab ta na kai harin ne a kan fararen hula da masu yawon bude idanu da kuma wadanda ba Musulmi ba. Sojojin kasar Kenyan na cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Afirka AMISOM da ke aiki a Somaliya.