1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Agajin abinci ga Somaliya

July 27, 2011

A larabar nan ce MƊD ke fatan fara jigilar kayayyakin abinci zuwa ƙasar Somaliya

https://p.dw.com/p/124jt
Sansanin bayar da agajin abinci a birnin Mogadishu, Somaliya, ranar Talata (26. 07. 2011).Hoto: dapd

Jami'ai daga shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya sun sanar da cewar a Larabar nan ce (27.07.11) suke fatan fara jigilar agajin abinci ta jiragen sama zuwa Mogadishu, babban birnin ƙasar Somalia. A da dai hukumar ta so fara jigilar ce a wannan Talata, amma ala-tilas ta jinkirta saboda matsalolin da ta fuskanta wajen tsara takardun da ake buƙata a ƙasar Kenya. Agajin, wanda ya haɗa da magungunan tallafawa waɗanda suka galabaita saboda matsalar nyunwa na da nufin ceto ɗimbin mutanen da ke fuskantar matsalar tamowa ne a yankin kusurwar gabashin Afirka.

Fari mafi muni cikin shekaru 60 ne dai ke addabar yankin, kuma hakan ya tilastawa dubbanin jama'a tserewa daga matsugunan su domin neman abinci da ruwa. Ƙoƙarin da wasu ƙungiyoyin bayar da agaji suka yi na kai ɗaukin abinci ya fuskanci turjiya daga ƙungiyar mayaƙan al-Shabab, wadda ke da iko a mafi rinjayen yankunan dake tsakiya da kuma kudancin ƙasar ta Somalia.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu