AI: 'Yan banga na kashe Fulani a Burkina
March 20, 2020kungiyar Amnesty International ta bayyana shaidu da ke nuna cewa wasu kungiyoyin 'yan banga na da aihakkin kisan mutane 43 da aka yi a cikin wasu kauyuka Fulani da ke arewacin Burkina Faso a ranar 8 ga Maris. Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Jumma'ar, kungiyar da ta himmata wajen kare hakkin bil Adama a duniya ta ce ta gano daga hirarrakin da ta yi da wadanda suka tsira da ransu cewa 'ya'yan kungiyar kato da doga ta Koglweogo ne ke da alhakin kashe-kashen.
'Yan adawar Burkina Faso sun bukaci da aka kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano abin da ya faru. Arewacin Burkina Faso dai ya fuskanci hare-haren ta'addanci a kai a kai a 'yan watanni baya-bayannan. Sannan tashe-tashen hankula sun yawaita tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma. Su kuwa kungiyoyin da ke da'awar jihadi sun kashe mutane sama da 800 cikin shekaru biyar na baya-bayannan a Burkina Faso.