Al-Ka'ida ta kai hari a Burkina Faso
February 28, 2017Talla
Kawo yanzu babu rahotannin asarar rai daga harin, sai dai an samu jikkatar wata jami'ar 'yan sanda. Wannan harin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da birnin na Ouagadougou ke cike tsauraran matakan tsaro, ganin manyan baki na halartar bikin baje kolin fina-finan Afirka. Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai, na ci gaba da zama barazana ga kasar Burkina Faso, inda ake yawaita kai hare-hare da yin garkuwa da mutane. A watan Disemban da ta gabata kungiyar Ansarul Islam, ta yi ikirarin kai harin da ya hallaka dakarun soji 12 a kan iyakar kasar da Mali. A yanzu dai hukumomin kasar na ci gaba da zurfafa bincike dan gano mabuyar mayakan.