Somaliya ta fuskanci harin kuna bakin wake
January 22, 2016Talla
Shaidun gani da ido sun tabbar da cewa daga bisani wasu 'yan bindiga sun bude wuta tare da yin harbin kan mai uwa da wabi da kuma yin garkuwa da baki dayan mutanen da ke gidan cin abincin. Wannan hari dai shi ne mafi muni da kasar ta fuskanta cikin wannan shekara. Wani jami'in dan sandan birnin na Mogadishu Mohamed Abdirahman da ya tabbatar da harin ya shaidar da cewa akalla mutane 20 ne suka hallaka ciki kuwa har da mata da kananan yara a abin da ya bayyana da rashin imani. Rundunar 'yan sandan kasar dai ta ce ce tuni aka kawo karshen garkuwa da mutanen da 'yan bindigar suka yi. Tuni dai kungiyar al-Shabaab ta masu kaifin kishin addini da ta addabi kasar ta Somaliya tsahon shekaru ta dauki alhakin harin.