Al-Shabaab ta kai hari a Somaliya
January 25, 2017Talla
Raahotanni dai sun nunar cewa mayakan na al-shabaab sun yi amfani da wata mota ne da ke makare da bama-bama wajen fasa kofar shiga otel din mai suna Otel Daya da ke kusa da majalisar dokokin kasar wanda kuma 'yan siyasa ke yawan zuwa can. Daga cikin wadanda suka jikkatan kuwa har da wasu 'yan jarida guda hudu wadanda suka je domin daukar rahotonni.