Bam ya kashe mutane 10 a Mogadishu
November 9, 2018Talla
Hare-haren sun auku ne a kusa da Sahafi Otal da ke dab da hedikwatar 'yan sanda a babban birnin kasar Mogadishu. Jami'an tsaro a Somaliya sun tabbatar da bindige maharan hudu da suka yi yunkurin shiga ginin Otal din. Shedu sun tabbatar da ganin gawarwakin mutane a kan titi jim kadan bayan harin. Tuni dai kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken. Kasar Somaliya na fuskantar munanan hare-hare daga kungiyar al-Shabaab da ke sanadiyar mutuwar fararen hula da jami'an tsaro.