Al-Shabaab ta kai wani sabon hari a Somaliya
September 18, 2015Talla
Kungiyar dai ta kwace akalla garuruwa uku a Kudanci da kuma tsakiyar Somaliya. Ko da a cikin watan da ya gabata ma kungiyar ta kai wani hari a sansanin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Afirka da ke yankin Janale tare da hallaka sojojin Uganda akalla 12.
A jiya Alhamis kungiyar ta samu nasarar kwace garin na Janale da ke da nisan kimanin kilomita 90 da kudancin Mogadishu babban birnin kasar. Tuni dai jami'an tsaron Somaliya da kungiyar ta Al-shabaab suka tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai gwamnatin Somaliyan ta yi watsi da nasarar da al-shabaab din ke samu ta na mai cewa garuruwan da ta sake kwacewar ba wasu masu muhimmanci bane.