1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamun samun kwanciyar hankali a Burkina Faso

Yusuf BalaSeptember 23, 2015

Shugaban mulkin rikon kwarya da sojoji suka hambarar a makon jiya Michel Kafando ya sanar da sake komawa kan kujerarsa inda aka yi wani karamin biki.

https://p.dw.com/p/1Gc7k
Burkina Faso Michel Kafando Staatspräsident hält Rede in Ouagadougou
Michel Kafando lokacin da yake jawabi bayan mayar da shi kan mulkiHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Takaitaccen bikin sake karbar mulkin na Michel Kafando da Firaminista Yacouba Isaac Zida dai ya samu halartar wakilai na jam'iyyun siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu da sojoji sai dai babu Janar Gilbert Diendere wanda aka gano ya tarbi tawagar shugabanni daga kungiyar ECOWAS a Ouagadougou dan shiga tsakani.

A cewar Michel Kafando abin da ya faru a makon da ya gabata rashin fahimta ce, sai dai yanzu komai na bisa turba.

"Mun yi fafutika a lokaci mara dadi tare, mun kuma hadu a lokaci guda lokacin da muka samu 'yancin kanmu. Na kama aiki kuma zan ci gaba da jan ragamar wannan kasa a matsayin shugaban riko da duniya ta amince da shi. Aikin rikon kwaryar mulkin wannan kasa zai ci gaba da gudana daga wannan lokaci dan gudanar da aikin kasa."

Burkina Faso Putsch-Anführer Gilbert Diendere empfängt Mahamadou Issoufou in Ouagadougou
Jagoran 'yan juyin mulki Gilbert Diendere yana tarbar shugaba Mahamadou Issoufou na NijarHoto: Reuters/J. Penney

A cewar shugaban rikon kasar ta Burkina Faso Michel Kafando da aka yi garkuwa da shi a makon da ya gabata zai ci gaba da aiki ya zuwa lokacin da kasar za ta kafu bisa tafarkin demokradiyya a nan gaba.

Kawar duk barazanar da za ta kawo tarnaki

Karkashin abin da aka cimma da sojoji da suka jagoranci juyin mulkin kasar ta Burkina Faso dai a cewar shugaban rikon, kafin bayyanar masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, sun rattaba hannu kan yarjejeniya da za ta kawar da duk wani abu da zai iya jefa kasar cikin rudani. To ko za a iya cewa yanzu da aka umarci sojan gwamnati su koma bariki hakan zai kawo karshen wannan rikici.

Burkina Faso Armeeeinheit am Flughafen Ouagadougou
Sojojin Burkina Faso a filin jirgin saman OuagadougouHoto: Reuters/J. Penney

Farfesa Alexander Stroh masanin kimiyyar siyasa ne kuma kwararre kan nahiyar Afirka a jami'ar Bayreuth a nan Jamus na da wannan ra'ayi.

"Wannan baya nuna cewa babu sauran matsala kan irin kalubalen tashin hankali da kasar za ta iya fuskanta. An dai bukaci sojojin da ke zagaye da fadar shugabansu da su kauce, sannan masu biyayya ga gwamnati su koma bariki. Hakan na nufin mutane ne dai ba za su gamsu ba. Sun ja daga ido da ido amma wannan dai ba ya nufin za a saki jiki baki daya."

Yafiya ga sojojin juyin mulki shi ne mafi a'ala

A yayin tattaunawa kan rikicin na Burkina Faso a ranar Talata a shelkwatar kungiyar ECOWAS a Abujar Najeriya, ba a tabo batun yin afuwa ga sojojin da suka jagoranci juyin mulkin ba, ballantana batun ba wa masu goyon bayan tsohon shugaba Campaore dama a zaben da kasar za ta yi an an gaba. Amma a fadar Farfesa Alexander Stroh abu mafi muhimmanci na zama yin afuwa ga wadannan sojoji da suka jagoranci juyin mulkin.

"Daga tattaunawar sulhu ta farko a birnin na Ouagadougou ta nunar da cewa yin afuwa shi ne abu na farko idan har ana son dorewar zaman lafiya a kasar, kasancewar akwai wasu batutuwa kwance a kasa da suka jawo juyin mulkin, ba wai kawai abun da ya faru a kwanakin bayannan kawai ne ba."

Masanan dai na ganin cewa ba yadda za a yi Janar Diendere ya mika kai haka ba tare da an mutunta bukatunsa ba da zasu kare martabar jam'iyyar CDP ta tsohon shugaba Blaise Compaoré kuma abun da ya faru zai sa a kuma dage zaben.