Al'amura sun fara kai wa 'yan ƙasar Somaliya iya wuya
December 23, 2011A yau dai zamu fara ne da rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wacce ta bayyana mamakinta a game da yadda ɗan hamayyar ƙasar Kongo Etienne Tshisekedi ya gabatar da kira ga magoya-bayansa da su ta da zaune tsaye bayan da kotun koli ta ƙasar ta tabbatar da nasarar shugaba mai ci Joseph Kabila a zaben Kongon da aka gudanar watan da ya gabata a kuma daidai lokacin da ake bikin rantsar da shugaban domin wa'adi mulki karo na biyu. Jaridar ta ce:
"Tshisekedi dai yayi iƙirarin lashe zaɓen da goyan bayan kashi hamsin da huɗu cikin ɗari na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa, amma kuma ba ya da wata shaida game da hakan. Ɗan hamayyar ma dai wuce makaɗi da rawa yayi, inda ya ware ladar kuɗi da zai ba wa duk wanda ya cafke Kabila ya kuma kawo shi gabansa a cikin ankwa. Ta haka Tshisekedi ya ci gaba da take-takensa na yaƙin neman zaɓe, inda yake kira ga 'yan ƙasar Kongo da su shiga ta da zaune tsaye."
A cikin nata rahoton, a lokacin da ta leƙa Somaliya, jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:
"A halin yanzun dai al'amura sun kai wa al'umar Somaliya iya wuya. Domin kuwa kusan dukkan ƙasashe maƙobta a yanzu suna wa ƙungiyar Al-Shabab taron dangi ne a ƙasar kuma babu wata alamar cimma zaman lafiya. Su kansu 'yan somaliyan ma dai a ganinsu gwamnatin da aka naɗa ƙarƙashin jagorancin Sharif Sheikh Ahmed tun a shekara ta 2009 ba ta da wani alfanu ga ƙasar."
Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta leƙa Somaliyar inda ta gano wani sabon salo na yaƙin cacar baka da aka shiga tsakanin sojojin Kenya da dakarun Al-Shabab ta kan yanar gizo. Ta ce dukkan sassan biyu na ƙalubalanta da cin mutuncin juna ne ta amfani da hanyar sadarwa ta Twitter a yanar gizo.
A daidai lokacin da ake fatan cewar ƙasar Mali zata iya zama abin koyi wajen daidaita al'amuranta domin su dace da canje-canjen yanayin duniya, amma fa ana fuskantar barazanar ɓillar wata mummunar masifa a yankin sahel da ka iya rutsawa da ƙasar, kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:
"Ƙasar Mali na fama da bala'in canje-canjen yanayi, kuma taron duniya akan makomar yanayin da aka gudanar a Durban baya-bayan nan bai tsinana mata kome ba. Taimakon kuɗi na euro miliyan goma da ministan kare muhalli na Jamus Norbert Röttgen yayi wa ƙasar, ba abu ne da ya taka kara ya karya ba dangane da fatan da ake yi na cewar Mali ka iya zama abin koyi a fafutukar daidaita al'amuranta da matsalar canjin yanayin duniyar."
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Umaru Aliyu