1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cajar waya guda don amfanin wayoyin smartphone

Ramatu Garba Baba
September 23, 2021

Tarayyar Turai na shirin samar da sabuwar cajar waya mai iya amfani da kowanne irin samfurin wayan smartphones da ake kerawa a nahiyar.

https://p.dw.com/p/40liv
Xiaomi Handy
Hoto: REUTERS/Anindito Mukherjee

Kungiyar tarayyar Turai ta sanar da shirin samar da cajar waya guda ga kowane irin waya, tsarin zai gindaya wa kamfanonin wayoyin-komai-da-ruwanka ko smartphones samar da cajar bai daya da kowanne waya ka iya amfani da ita. Baya ga kawo sauki ga rayuwar jama'a da ke kashe kudi don mallakar caja, EU na ganin, tsarin zai taimaka wajen rage yawan sharar cajar wayoyi da ake zubarwa a duk shekara.  

Tuni dai kamfanin Apple mai kera samfurin iphones, ya nuna yadda matakin ke tattare da wasu kalubale da za su iya rage wa wayoyinta armashi. An bai wa kamfanonin wayoyin salulan shekaru biyu domin kintsawa kafin soma aiki da sabon tsarin. Dokar za ta shafi wayoyin da ake sayarawa a kasashen nahiyar Turai 30 kadai.