Tattauna batun sauyin yanayi
June 15, 2021Talla
Amirka da shugabannin kungiyar tarayar Turai za su gana da zummar tattaunawa a kan batun dumamar yanayi da ke ci gaba da yi wa duniya barazana.
A wannan taron ne za su tsaida ranar da za a daina amfani da makamashin kwal a cewar sanarwar da bangarorin biyu suka fidda.
Haka zalika shugaban na Amirka Joe Biden zai gana da shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai Ursula von der Leyen gami da shugaban majalisar Turai Charles Michel domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi cinikayya da ma annobar Covid-19.
Wannan ganawar dai na zama zahiri a kan komawar alaka tsakanin kungiyar ta Turai da Amirka musamman ma na batun yaki da dumamar yanayi da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya fidda kasar daga yarjejeniyar da aka cimma a can baya.