Amirka da Turai sun cimma matsaya
June 15, 2021Amirka da Turai sun cimma nasara a warware daddadiyar takaddamar cinikayya da ke tsakaninsu kan jiragen sama kirar Beoing da Airbus. Shugabar hukumar Kungiyar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen da ta wakilici yankin a ganawa da Shugaba Joe Biden, ta ce an soma ganawar da kafar dama, inda nan take suka amince kan a soke duk wasu tara da haraji da suka janyo jayayya, za su kuma mutunta wannan yarjejeniyar har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Von Der Leyen, ta ce wannan ya ba su damar bude sabon babi bayan kwashe shekaru akalla 17 ana takaddama. Wannan na zuwa ne, bayan babban taron shugbbanin kungiyar tsaro ta NATO a birnin na Brussels, inda a karon farko Shugaban Amirka Joe Biden ke halarta tun bayan maida kasarsa a cikin kungiyar da tsohon Shugaba Donald Trump ya fidda. Shugaba Biden zai tattauna da sauran shugabanin kungiyar a kan bukatar daukar matakan hadin kai domin dakatar da barazanar da kasashen China da Rasha ke yi.