Amirka ta kashe wani kusa na al-shabaab
December 30, 2014Wani babban mai fada a ji a kungiyar al-Shabaab dake gaggwarmaya da makamai a Somaliya ya rigamu gidan gaskiya a wani harin da jiragen yakin Amirka suka kadamar. Hukumar leken asiri Somaliyar da ta yi wannan bayani a cikin wata sanarwa, ta cebisa taimakon dakarun wnanan kasa ne dakarun na Amirka suka yi wannan nasara.
Tun a jiya Litinin ne dai ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagone ta yi ikirarin kai hari ta sama a Somaliya, da nufin ganin bayan daya daga cikin shugabannin al-Shabaab da ake nema ruwa a jalo. sai dai sun bayyana cewa suna gudanar da bincike don tabbatar da cewa hakarsu ta cimma ruwa.
Ita dai gwamnatin Somaliya ta bayyana cewa ba wani aka kashe ba illa Abdichakour da aka fi sani da suna Tahlil, wanda shi ne ya jagoranci rukunin 'yan al-Shabaab da suka kai jerin hare-hare a Mogadischo babban birnin kasar ta Somaliya.