1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadin Amirka kan balaguro a Burkina Faso

Gazali Abdou Tasawa
November 27, 2019

Amirka ta gargadi 'yan kasarta da su kauracewa yin balaguro zuwa kasar Burkina Faso a sakamakon karuwar ayyukan ta'addanci da na sace-sacen jama'a da sauran muggan ayyuka.

https://p.dw.com/p/3Tnda
Afrika Burkina Faso  l Militär
Hoto: DW/F. Muvunyi

 A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fitar a jiya Talata ta ce a yanzu kasar ta Burkina Faso ta kai kololuwar hadari ga matafiya. A shekarun baya dai Burkina Faso na daga cikin kasashen da 'yan yawan buda ido ke yawan kai ziyara.

To sai dai tun daga shekara ta 2015, ana fuskantar sace-sacen jama'a ko yin garkuwa da su don neman kudin fansa, da ma hare-haren kungiyoyin masu da'awar jihadi.

 MDD ta kiyasta cewa daga farkon shekara ta 2015 zuwa yau,  Mutane kimanin 700 suka halaka wasu kimanin dubu 500 suka tsere daga gidajensu a kasar ta Burkina Faso a sakamakon hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda.