Zargin kashe 'yan IPOB a Najeriya
August 5, 2021A rahoton na kungiyar ta Amnesty International dai, akwai bayanan cewar jami'an tsaron Najeriyar sun yi amfanin da karfin tuwo wajen kashe 'yan rajin kafa kasar Biafran na IPOB kimanin 115 a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kungiyar kuma da Nnamdi Kanu da yanzu haka ke fuskantar shari'a a Najeriyar ke jagoranta. Wadannan kashe-kashe dai a cewar kungiyar, sun afku ne yayin da 'yan rajin kafa kasar Biafran suka matsa lamba a yankin musamman a farkon wannan shekara da mu ke ciki ta 2021.
Karin Bayani: Umarnin da IPOB ta bayar ya karbu a Najeriya
Ko da yake kungiyar ta Amnesty International ta nunar cewar a rikicin da ya afku cikin watanni hudu kacal bisa alkaluman da 'yan jaridu a Najeriyar suka bayar, yayin da adadin jami'an tsaron da suma suka rasa rayukansu ya kai 21 baya ga kone ofisoshin 'yan sanda 20 da kuma wasu ofisoshin hukumar zabe da ke yankin. Kungiyar ta kuma bayyana cewar abin da ya afku din, tsananin take hakkin dan Adam. Tuni dai 'yan kungiyar ta IPOB suka mayar da maratani kan rahoton, yayin da DW ta yi kokarin jin ta bakin jami'an 'yan sanda, sun nunar da cewa za su fitar da sanarwa dangane da rahoton.