1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta bayyana damuwa da kisan fararen hula

Uwais Abubakar Idris
January 30, 2018

A Najeriya kungiyar kare hakin jama’a ta Amnesty International ta baiyana damuwa kan harin da sojoji suka kadammar ta sama domin kwantar da rigingimu tsakanin makiyaya da manoma wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 168.

https://p.dw.com/p/2rm43
Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: NPR

Kungiyar ta Amnesty International ta nuna damuwarta ne a kan abinda ta kira wuce iyaka da ake yi wajen maida martani a kan  tashe-tashen hankula da ake fama da su ta hanyar amfani da hare-haren jiragen sama a rikicin Fulani makiyaya da manoma abinda tace ba za’a amince da shi ba.

Ein von Boko Haram zerstörtes Dorf in der Nähe von Rann
Hoto: DW/A.Kriesch

Kama daga Jihohin Adamawa da Taraba da Benue da Kaduna da Ondo inda aka fuskanci irin wannan rikici, ta ce hanyoyin da gwamnatin ke bi wajen kwantar da rigimar na wuce iyaka, domin bayan jinkirin daukar mataki daga gwamnati, yawan mutanen da suka mutu da watan Janairun bana kadai suka kai 168, duka a kokarin kwantar da tarzoma a cewar Mallam Isa Sanusi manajan yada labaru na Amnesty International.

Symbolbild Nigeria Luftwaffe
Jirgin mai saukar ungulu na sojin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Amnesty International ta ce tana da shiadu na gani da ido a kan yadda jiragen saman yaki da mai saukan ungulu suka harba makamai a kan mutanen da ke kokarin tsira daga harin da aka kai musu, amma sojojin ke bayyana cewa an yi hakan ne don bada tsoro ga masu tada rikici. Osai Ojigbo darakta a kungiyar yace kadammar da hare-hare ta sama ba hanya ce da aka amince da ita ba a kowane mataki.

Tuni dai rundunar sojan saman Najeriya ta musanta cewa ta aikata duk wani laifi na take hakkin jama’a a kan wannan lamari kamar yadda Air Vice Marshal Olatokunboh Adesnya kakakin rundunar ya baiyana.

Von Boko Haram zurückgelassener Panzer in Yola, Adamawa, Nigeria
Wata unguwar al'umma a Adamawan NajeriyaHoto: picture alliance/AA/M. Elshamy

‘’Rundunar sojan saman Najeriya ta yi mamaki kungiyar Amnesty International za ta samu irin wannan bayani maimakon ta tuntubemu sai kawai ta je ta buga wannan rahoto, ya kamata ta bincika. Mu bamu taba kai hari muka kashe wani a wannan lamari ba.’’

Sai dai kungiyar Amnesty ta ce akwai bukatar gudanar da bincike a tsanake. Amma ga Mallam Kabiru Adamu masani a fanin tsaro ya ce akwai muhimmin abu daga wannan sako.

Kungiyar Amnesty dai ta dade ta na zargin jami’an tsaron Najeriya da laifufukan take hakkin jama’a wanda a karon farko gwamnatin ta kafa kwamitin da ke bincike a kan lamarin, wanda ake jiran samakamo da kuma matakin da za ta dauka.