An bayyana sunayen 'yan takara a Burkina Faso
August 30, 2015Talla
A cikin yan takara 22 da aka yi rejista, majalisar ta yi watsi da takarar wasu jama'ar guda shida, a ciki har da ta Ɗan takarar jam'iyyar CDP Congres pour la Democratie ta tsohon shugaban ƙasar wato Blaise Compaoré, ,da kuma wasu shugabannin jam'iyyuin siyasar waɗanda suka yi ƙawance da tsohuwar jam'iyysar da ta yi mulkin wanɗanda suka rufa wa Compaoré, baya ya yi tazarce.
A cikin watan Afrilu da ya gabata aka amince da wata dokar a ƙasar ta haramta wa waɗanda suka goyi bayan tsohon shugaban ya yi wa kudin tsarin mulkin kwaskorima domin tsayawa takara a wa'adi na uku duk kuwa da cewar doka ba ta amince da haka ba kafin daga bisanni titi ya korishi daga mulkin a cikin watan Oktoba shekarar bara.