An dage zaben shugaban kasa a Somaliya
December 27, 2016Talla
Kasar Somaliya ta sake dage zaben shugaban kasa a karo na hudu sakamakon fargabar tursasa wa jama'a da kuma magudin zabe. A gobe Laraba ya kamata a gudanar da zaben, amma kuma wani babban jami'i da ke kula da harkokin zabe na kasar ya bayyana wa manaima labarai cewar za a jinkirtashi har i zuwa karshen watan Janairu.
Bisa ga tsarin kasar Somaliya dai ba kai tsaye talakawa ke zaban shugaban kasa ba. Suna zaben 'yan majalisa ne, wadanda su kuma alhakkin zaban shugaban kasa ya rataya a wuyansu.
'Yan adawan Somaliya sun nuna damuwa dangane da dage-dage zaben na shugaban kasa, lamarin da a cewarsu ke nuna shirin gwamnati na murda wannan zabe.