1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza cimma matsaya a taron kolin EU

Binta Aliyu Zurmi
May 7, 2021

Batun janye hakkin mallaka kan fasahar hada rigakafin corona ya raba kawunan shugabannin kasashe a taron kolin kungiyar EU

https://p.dw.com/p/3t7vp
Portugal EU-Gipfel
Hoto: Estela Silva/AP Photo/picture alliance

An sami rarabuwar kawuna a taron kolin kasashen EU. Takadamar da ta barke a kan janye hakkin mallaka na fasahar hada rigakafin cutar corona da wasu kamfanoni suka samar domin ba da dama ga sauran kamfanoni su yi rigakafin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kaso dari cikin dari na allurar da Amirka ke samarwa na a cikin kasarta ba ta ba ma kowa, yace janye ikon mallaka ba shi ne abin da ya kamata a maida hankali a kai ba a wannana lokacin. Macron ya ce raba fasahar samar da rigakafin shi ne abin dubawa.

Firaministan kasar Poland ya ce za su ci gaba da matsawa kasashen da ke da wannan ikon mallaka har sai sun fidda shi domin kasashen da ke da iko su ma su shiga hada nasu rigakafin.

An dade dai ana zargin kasashen EU da Amirka da ma wasu da ke samar da rigakafin da boye su, ba tare da waiwayar sauran kasashen duniya ba.