Burkina Faso: 'Yan bindiga sun kashe mutane 15
April 28, 2021Bayanin kashe-kashen ya fito sun fito ne a ranar Talata amma acewar wani shugaban siyasa da ya bukaci kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya sakaya sunansa, tun a ranar Litinin da daddare 'yan bindigar suka kai samamen a wasu kauyukan yankin Seytenga na kasar. Jami'in ya ce 'yan bindigar sun fara kashe mutane 10 a kauyen Yatakou sannan sai suka matsa kauyen Sofokel inda suka halaka mutum biyar.
Jami'an tsaron Burkina Fason sun tabbatar da labarin, sai dai ba su bayar da adadin mutanen da 'yan bindigar suka halaka ba. Tuni ma dai hukumomi suka tura da karin jami'an tsaro amma kuma duk da haka lamarin ya sanya mutanen yankin na Seytenga kaurace wa gidajensu.
Wadannan kashe-kashe dai na zuwa ne a yayin da aka sanar da kashe wasu Turawa 'yan jarida guda uku a Burkina Faso a wani hari da aka kai wa wata tawagar masu gangamin yaki da farautar dabbobi a cikin dazuka.