Sojojin Burkina masu yawa sun halaka
August 20, 2019Talla
A cikin wata sanarwa da rundunar sojojin kasar ta Burkina Faso ta fitar inda ta bayyana harin a matsayin mafi muni da sojojin gwamnatin suka fuskanta a cikin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin, ta ce tana fargabar adadin sojojin da suka mutu a cikin harin na Soum da ke a arewacin kasar ya haura 20 ta la'akari da yadda ya zuwa yanzu ba a da duriyar da dama daga cikinsu.
Sai dai rundunar sojojin kasar ta Burkina Faso ta ce ta yi nasarar halaka da dama daga cikin maharan bayan da ta yi amfani da jiragen yaki da kuma kaddamar da wani farmaki ta kasa domin farautar maharan bayan aukuwar harin.