An jefi tawagar Macron a Burkina Faso
November 28, 2017Talla
Mai magana da yawun gwamnatin Faransa ya bayyana cewa an jefi motar mambobin wata tawaga da ke bin bayan Shugaba Emmanuel Macron a ziyararsa zuwa Burkina Faso.
Bruno Roger-Petit ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa lamarin ya faru ne a yayin da a bangare guda kuma Shugaba Macron da takwaransa Roch Marc Christian Kabore na can suna tattaunawa. Har iala yau lamarin na faruwa yayin da ake tsammanin Macron zai yi babban jawabinsa a jami'ar Ouagadougou, duk da fargaba da ake da ita ta samun zanga-zanga ta masu bore. Gwamnatin ta Burkina Faso dai ta bada umarni a rufe makarantu don samun sauki na samar da tsaro da rage kai kawo ababan hawa.