1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan dakarun kiyaye zaman lafiya a Somaliya

Suleiman BabayoSeptember 1, 2015

Tsagerun kungiyar al-Shabaab na Somaliya sun kai hari kan sansanin dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka

https://p.dw.com/p/1GPa6
Al-Shabaab Kämpfer in Mogadishu
Hoto: picture-alliance/landov

Tsagerun kungiyar al-Shabaab masu kaifin kishin addinin Islama na Somaliya sun kai hari kan sansanin dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka da ke yankin kudancin kasar. Rahotannin sun nuna cewa sojoji da dama sun gamu da ajalinsu yayin farmakin daruruwan tsagerun da safiyar wannan Talata.

Sai dai wata sanarwar dakarun kiyayen zaman lafiyar ta karyata ikirarin kungiyar al-Shabaab bisa kwace ikon da sansanin wanda yake da nisan kilo-mita 80 kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar. Kawo yanzu babu adadin na yawan wadanda harin na tsagerun kasar ta Somaliya ya ritsa da su.