An kai hari kan wani coci a Burkina Faso
April 29, 2019Mahara sun halaka mutane biyar a wani harin da suka kai kan coci a Lardin Soum da ke arewacin kasar Burkina Faso, a daidai lokacin da mabiya addinin kirista ke tsakiyar ibadunsu. Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka mutu a harin har da limamin cocin, a yayin da wasu mutane biyu kuma suka bata ba tare da sanin inda suka shiga ba.
Shaidu sun ce maharan sun isa garin ne kan babura, inda suka yi ta harbe-harbe, kafin daga bisani suka bude wuta ga mutanen da ke cikin cocin. Haka kuma a ranar Jumma’ar da ta gabata, an kashe wasu mutane shida ciki har da malaman makarantar boko biyar a lardin Koulpélogo a gabashin kasar ta Burkina Faso.
Kawo yanzu akalla mutane 350 ne suka halaka sakamakon hare-haren ta’addanci a wasu bangarori na kasar Burkina Fason da ke fama da matsalar tsaro tun daga shekarar 2015.