1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wasu tsoffin sojin RSP a Burkina Faso

Salissou BoukariJanuary 24, 2016

An kama sojoji a kalla 11 na tsofuwar rundunar RSP masu tsaron lafiyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da ake zargi da satar makammai.

https://p.dw.com/p/1Hj89
Burkina Faso Machtübernahme General Honore Traore 31.10.2014
Hoto: Reuters/J. Penney

A ranar Jumma'a ce wasu suka kai hari ga wata ma'ajiyar makammai da ke kusa da birnin Ouagadougou inda suka yi awon gaba da wasu makammai. A cewar Komanda Mahamadi Bonkoungou shugaban kula da hulda tsakanin rundunonin sojan kasar ta Burkina Faso da wajejen karfe hudu ne dai na Asubahin ranar Jummaa da ta gabata wasu mutane gommai suka kai hari a wurin ajiyar makammai da albarussai abun da ya haddasa jin ciwon daya daga cikin sojojin da ke tsaron wurin, inda ya ce a halin yanzu suna neman wasu sojojin a kalla 15.

A hannu daya kuma daruruwan mutane ne suka gudanar da wani jerin gwano na lumana a birnin na Ouagadougou domin tunawa da wadanda harin ta'addancin da aka kai na ranar 15 ga wannan wata a Hotel Splendid ya rutsa da su, harin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane a kalla 30.