1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kame tsaffin ministoci a Burkina Faso

Yusuf BalaApril 7, 2015

Jam'iyyar adawa a kasar ta Burkina Faso ta bayyana kamen da cewa tozartawa ce ga mambobinta da masu rike da kasar ke yi.

https://p.dw.com/p/1F3pj
Michel Kafando Übergangspräsident Burkina Faso 17.11.2014
Hoto: AFP/Getty Images/Stringer

Mahukunta a kasar Burkina Faso sun cafke wasu tsaffin ministoci uku da suka yi aiki karkashin gwamnatin kama karya ta tshohon shugaba Blaise Compaore, kamar yadda jam'iyyarsu ta bayyana a ranar Talatannan. Kamen kuma da jam'iyyarsu ta bayyana da cewa tozartawa ce ga mambobinsu.

Tsofaffin ministocin dai su ne Jerome Bougoumada da ya rike ma'aikatar harkokin cikin gida da Jean Martin Ouedraogo da ya rike ma'aikatar da ke lura da harkokin samar da ababan more rayuwa, na uku kuwa Salif Kabore da ya rike ma'aikatar samar da albarkatun kasa.

Bayanin kamen dai na fitowa ne daga Leonce Kone jigo a tsohuwar jam'iyyar da ke mulkin kasar ta Burkina Faso CDP a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Wasu majiyoyin tsaro biyu sun tababbatar da kamen ministocin wanda suka ce ya faru ne tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata sai dai basu bada wani karin bayani ba.