Harin kan fararen hula a Burkina Faso
May 19, 2023Talla
Kungiyoyi masu dauke da makamai sun kai farmaki cikin garin Bilguimdure, wani kauye da ke cikin gundumar Sangha, a lardin Kulpélogo da ke a tsakiyya maso gabashin Burkina Fason mai iyaka da kasashen Ghana da Togo, inda suka kashe mutane goma. Kasar Burkina Faso, wacce ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a shekarar ta 2022, ta fada cikin tashin hankali na masu jihadi a shekara ta 2015. wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fararen hula da sojoji fiye da dubu goma.