An kashe mayakan al-Shabaab 100 a Somaliya
November 21, 2017Talla
A wata sanarwa da rundunar sojojin Amirka suka fitar, na cewa harin na hadin gwiwa ne da ya samu goyon bayan dakarun gwamnatin Samaliya a yunkurin kakkabe 'yan tawaye da ke barazana da rayuwar fararen hula da sojoji a Somaliya.
Sanarwar ta ce za a ci gaba da kai farmaki kan mafakar mayakan a duk inda suke a fadin kasar, Amirka dai na ci gaba da kaddamar da jerin hare-hare kan kungiyar al-Shabaab a cikin wannan shekara da nufin tabbatar da alkawuran shugaban Amirka Donald Trump na kakkabe tsagerun kungiyoyi masu tsauraran akidu a gabashin Afirka.