An kashe 'yan sandan Burkina Faso
October 6, 2018Talla
Lamarin da ya auku a garin Solle da ke kan iyakar kasar da Mali, ya faru ne cikin daren da ya gabata, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.
Maharan da farko sun buda wuta ne kan ayarin motocin 'yan sandan, kafin su hau kan wasu nakiyoyi da suka daddasa.
Akwai ma wasu 'yan sandan da dama da rahotanni suka ce sun jikkata a lamarin.
Harin ya zo ne kasa da mako guda da wasu maharan suka yi wa wasu sojojin kasar kofar rago, tare da kashe shida daga cikinsu a gabashin Malin.