SiyasaJamus
Sojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 70
April 17, 2022Talla
Kakakin rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabkwet, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar an kaddamar da luguden wuta kan mayakan ne bayan da aka tantance maboyarsu ciki har da wani sansanin atisayen da mayakan ke amfani da shi a kauyen Tumbun Rego da ke yankin Tafkin Chadi a ranar 14 ga wannan wata.
A baya-bayan nan dai runudunar tsaron ta Najeriya ta tsananta kai farmaki a kan mayakan masu da'awar jihadi a yankin Arewa maso gabashin kasar, tare da kara matsa kaimi ga 'yan fashin daji da masu garkuwa da jama'a da suka yi kaka gida a jihohin Arewa maso yammacin kasar, inda kuma ta ce tana samun nasara.