1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo ƙarshen matsalar yunwa a Somaliya-Majalisar Ɗinkin Duniya

February 3, 2012

Sai dai da sauran rina a kaba matuƙar ba bu nagartattun matakan samar da abinci na lokaci mai tsawo.

https://p.dw.com/p/13wir
Somali children enjoy a liquid food drink provided by a local NGO in the port town of Kismayo, Wednesday, Sept. 12, 2007, where more than eight thousand Children live in camps. The Somali health minister and UNICEF warned on Wednesday that thousands of children were facing starvation as violent attacks continued around the south of the country, "We have been receiving reports of an alarming rate of malnutrition in southern Somali regions, where thousands of children are on the verge of death," said Health Minister Isse Weheliye. (AP Photo/ Nasteh Dahir Farah)
Hoto: AP

Ƙungiyar abinci da aikin noma ta duniya wato FAO ta ayyana kawo ƙarshen matsalar yunwa a ƙasar Somaliya. Babban daraktan hukumar Jose Graziano da Silva ya nunar a birnin Nairobi na ƙasar Kenya cewa ruwan sama da aka fara samu da shiga aikin noma gadan gadan da kuma taimakon jin ƙai da ƙasashen duniya suka bayar a cikin watanni shida da suka wuce su ne manyan dalilan wannan ci-gaba da aka samu.

"Muna da tanadi na watanni uku na rigakafin duk wata matsalar yunwa da za ta sake kunno kai sakamakon kamfar ruwa. Muna bukatar zaman lafiya a Somaliya domin kawar da yunwa a yankin. Muna neman taimakon Ubangiji."

Sai dai duk da wannan ci-gaban da aka samu da sauran rina a kaba, domin har yanzu yankin ƙahon Afirka na fuskantar barazanar fari, idan ba a ɗauki ƙwararan matakan samar da abinci na dogon lokaci ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu