An kawo ƙarshen matsalar yunwa a Somaliya-Majalisar Ɗinkin Duniya
February 3, 2012Ƙungiyar abinci da aikin noma ta duniya wato FAO ta ayyana kawo ƙarshen matsalar yunwa a ƙasar Somaliya. Babban daraktan hukumar Jose Graziano da Silva ya nunar a birnin Nairobi na ƙasar Kenya cewa ruwan sama da aka fara samu da shiga aikin noma gadan gadan da kuma taimakon jin ƙai da ƙasashen duniya suka bayar a cikin watanni shida da suka wuce su ne manyan dalilan wannan ci-gaba da aka samu.
"Muna da tanadi na watanni uku na rigakafin duk wata matsalar yunwa da za ta sake kunno kai sakamakon kamfar ruwa. Muna bukatar zaman lafiya a Somaliya domin kawar da yunwa a yankin. Muna neman taimakon Ubangiji."
Sai dai duk da wannan ci-gaban da aka samu da sauran rina a kaba, domin har yanzu yankin ƙahon Afirka na fuskantar barazanar fari, idan ba a ɗauki ƙwararan matakan samar da abinci na dogon lokaci ba.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu