SiyasaAsiya
An kona gawar tsohon Firaministan Indiya
December 28, 2024Talla
An dai gudanar da jana'izar Manmohan Singh bayan kammala wasu al'adu da tsatsube-tsatsube na mabiya addinin Sikh a Indiya. Firaministan ya gudanar da mulki na ba yabo ba fallasa da hakan ya sanya kafa kawancen siyasa a kasar tare da barin mulki a 2014, bayan shan kaye daga Neranda Modi. Firaminista Modi na daga cikin wadanda suka halarci kona gawar shugaba Singh, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen shugaba.
Karin bayani:Tsohon Firaministan Indiya Manmohan Singh ya rasu
Shugabannin kasashen Amurka da Canada da Sri Lanka da China da Pakistan na daga cikin wadanda suka nuna alhini na mutuwar Manmohan Singh wanda suka bayyana shi a matsayin wanda ya bada gudummuwa a diflomasiyyar duniya.