1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba a Hong Kong

Abdul-raheem Hassan
July 1, 2019

'Yan sandan sun yi amfani da kulake da hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zangar adawa da bikin cika shekaru 22 da hadewa Hong Kong da China da suka mamaye tituna da harabar gidan gwamnati.

https://p.dw.com/p/3LNch
Proteste in Hongkong
Hoto: Getty Images/AFP/V. Prakash

Masu zanga-zangar sun yi zaman dirshan domin hana jama'a halartar bikin cika shekaru 22 da komawar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar China. Jack na cikin masu zanga-zangar."Muna cikin damuwa, muna da 'yancin yin zanga-zanga domin kare yankinmu. Ban san me ya sa gwamnati ke cutar da mu ba, wannan yi wa dimukuradiyya zagon kasa ne, tsarin doka shi ne mataki na karshe tsakaninmu da gwamnatin China."

A kowace ranar 1 ga watan Yuli al'ummar Hong Kong na gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar China, sai dai a bana lamarin ya tsananta, ganin yadda yankin na Hong Kong ke fuskantar bore kan kudurin doka mai sarkakiya da ke neman a hukunta 'yan Hong Kong da suka yi laifi a kasar China.