An nada sabon Faraminista a Somaliya
November 24, 2007Talla
Majalisar dokokin ƙasar Somaliya ta rantsar da Mr Nur Hassan, a matsayin sabon Faraministan Gwamnatin rikon ƙwarya ta ƙasar. Rahotanni sun nunar da cewa Nur Hassan ƙwararre ne a fage na tafiyar da harkokin mulki. Kafin ɗarewa sabon muƙamin, Mr Nur Hassan na riƙe da matsayin mataimakin shugaban ƙungiyyar agaji ta Red crescent ne a ƙasar. Masu nazarin siyasa na kallon naɗin na Mr Hassan, a matsayin wata kafa ce da za ta taimaka wajen warware rikicin siyasa da ƙasar ke fama da ita. An dai zargi tsohon Faraministan ne, wato Ali Mohammed Gedi da gaza shawo kan rikice- rikicen dake a tsakanin ƙabilun ƙasar ne.