An naɗa wakilin AU a Somaliya
October 9, 2010Talla
Shugaban komitin haɗin-gwiwa na Ƙungiyar Gamayyar Afirka(AU), Jean Ping ya naɗa tsofon shugaban ƙasar Ghana, Jerry John Rawlings a masayin wakilin ƙungiyar na musamman a ƙasar Somaliya. Shugabannin ƙasahen Afirka ne dai suka ummarci Ping da ya naɗa wakili na musammun a kasar ta Somaliya wacce ke fama da tashe-tashen hankula da suka ki ci suka ki canyewa, domin kara gaggauta yunƙuri samar da zaman lafiya. Wannan naɗi dai na Rawlings, wanda ya jagoranci Ƙasar Ghana daga shekara ta 1981 zuwa shekara ta 2000, ya zo ne a daidai lokacin da dakarun ƙungiyar na AMISOM ke ci gaba da gwabza faɗa da ƙungiyar 'yan tawaye na Al-Shabab a ƙasar da marabinta da gwamntin tun a shekara 1991.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas