1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi Kenya ta sake tunani kan Dadaab

Ahmed SalisuApril 14, 2015

Hukumar kula 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kasar Kenya da ta sake tunani kan yunkurin ganin an rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab.

https://p.dw.com/p/1F7ti
Flüchtlingslager Dadaab Kenia
Hoto: AP

Hukumar ta ce idan har aka kai ga rufe sansanin, hakan na iya jawo kalubale babba ga kasar ta Somaliya wadda dama ke fama da tada kayar baya ta 'yan bindiga kazalika mazauna sansanin da Kenya din ke son su koma gida ka iya shiga wani yanayi maras kyau.

Mai magana da yawun hukumar ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen ganin an tabbatar da doka da oda a Dadaab wanda hakan zai hana masu son tada zaune tsaye aiwatar da hare-hare a cikin kasar ta Kenya.

A ranar Asabar din da ta gabata ce mahukuntan Kenya din suka baiwa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wa'adin watanni uku na su rufe sansanin, abinda da dama ke kallo a matsayin martani kan harin jami'ar nan ta garin Garissa da 'yan al-Shabaab suka kai har ma suka hallaka dalibai kusan 150.