1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki dan jaridar Jamus da aka yi garkuwa da shi a Somaliya

September 23, 2014

Bayan kwashe shekaru biyu a hannun masu garkuwa da jama'a a Somaliya wani dan jaridar Jamus ya kubuta

https://p.dw.com/p/1DJGs
Somalia Soldaten
Hoto: dapd

Wata mujalla da ke fita a mako-mako a kasar Jamus Der Spiegel ta bayyana cewa dan jaridar dan asalin Jamus da Amurka da aka yi garkuwa da shi shekaru biyu ke nan a Somaliya, ya zuwa yanzu an sake shi.

Der Spiegel ta bayyana a shafinta na intanet cewa an dauki Michael Scoot Moore zuwa birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasarta Somaliya.

Moore wanda ke aike wa wannan mujalla ta Spiegel da rahotanni ya fada hannun masu garkuwa da mutane a lokacin da yake aiki kan wani littafi da aka rubuta kan masu fashi cikin teku a watan Janairu na shekara ta 2012.

Duk da cewa mujallar ba ta bayyana yadda ta kai dan jaridar ya kubuta ba, ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta Somaliya ta bayyana cewa "An sako dan asalin Jamus da Amurka da aka kama shi a Somaliya "

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo