An sako jami'an jiragen ruwa 21 a Somaliya
October 24, 2016Talla
Masu shiga tsakani na kasa da kasa dai sun ce an yi ta bata kashi tsakanin jami'an tsaro da 'yan fashin tekun kamin aka kai ga samun nasarar kubutar da mutane 21 da ake tsare da su a tun watan Mayu shekara ta 2012.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar China ta fitar na cewa akwai 'yan kasar ta 10 cikin wadanda aka ceto, kana wasu biyu daga kasar Taiwan. Sauran sun hada da 'yan kasashen Biyatinam da Kambodiya, da Indunisiya da Pilipin. Akwai dai rahotanin da ke cewa masu fashin tekun sun karbi dala miliyan daya da rabi a matsayin kudin fansa.
Fashi a Teku dai ya zama ruwan dare a Somaliya da ke zama babban kalubale na gudanar da harkokin kasuwanci na kasa da kasa da ke bukatar jigila ta hanyoyin ruwa.