An sako ba Amirken da aka sace a Nijar
March 20, 2023A watan Oktobar 2016 aka yi garkuwa da Jeffrey Woodke daga gidansa da ke Abalak a jihar Tahou bayan hallaka wasu masu ba shi tsaro da suka yi yunkurin hana tafiya da shi a yayin da aka yi garkuwa da dan jarida Olivier Dubois a kasar Mali.
Rahotanni sun ce, an kai Mista Woodke wanda ke aikin agaji a wancan lokacin kasar Mali inda ake zaton ya shafe wadannan shekarun, duk su biyun sun isa Yamai babban birnin Nijar a wannan Litinin. Dubois dan shekaru 48 da aka yi garkuwa da shi kusan shekaru biyu da suka gabata a yayin da Woodke ke da shekaru sittin da daya da haihuwa.
Fadar WhiteHouse ce ta sanar da labarin a wannan Litinin, amma ta ki yin karin haske kan ko an biya kudin fansa ko cimma wata yarjejeniya da wadanda suka sace wadannan mutanen biyu kafin sakinsu.