An sanar da sabbin ministoci a Birtaniya
July 25, 2019Tsohon magajin garin London wanda ya kama aiki a ranar Laraba (24.07.2019) ya sallami da dama daga cikin ministocin da suka yi aiki da tsohuwar Firaminsta Theresa May. Ya kuma nada Sajid Javid tsahon ma'aikacin bankin Deutsche Bank a matsayin ministan kudin kasar yayin da Dominic Raab mai goyon bayan ficewar kasar daga EU ya samu mukamin sakataren harkokin waje.
A baya dai masu goyon bayan ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai sun zargi Theresa May da yin ko in kula da bakutar wadanda suka kada kuri'un ficewar bayan ta dauki alwashin ganin harkar cinikayya ta ci gaba tsakanin Birtaniya da kasashen EU. An dai jiyo yadda Majalisar dokokin turai ta shardanta wa Birtaniya cewar ya zama wajibi a tantance 'yancin al'ummomi da cimma matsaya kan batun kudade da na tsaro da kuma batun iyakar Ireland tsakaninta da Kungiyar ta EU kafin cikar burin Birtaniya.